
Hukumar kula da magunguna da abinci ta kasa, NAFDAC ta yi gargadi cewa an shigo da maganin hana daukar ciki me suna Postinor na bogi Najeriya.
Hukumar tace ta tabbatar da hakan ne bayan da hukumar Society for Family Health (SFH) wadda itace aka yadda ta shigo da maganin ta bayyana cewa ba itace ta shigo da maganin boge din ba.
NAFDAC tace yanda za’a gane maganin na boge shine, rubutunsa kanana ne, sannan an yi kuskuren rubuta kalmar Verify inda aka rubuta Veify.
Sannan kuma akwai kuskuren rubutun Distnibuted in Nigeria maimakon a rubuta, distributed in Nigeria.
Hukumar tace wannan magani na jabu na nan yana yawo a Najeriya kuma akwai yiyuwar yana dauke da sinadarai masu cutarwa dan haka ta nemi a gujeshi.