An hango jirgin ruwa da tutar Najeriya a kasar Faransa.
Wani jirgin ruwa ya dauki hankulan ‘yan Najeriya bayan da aka hangoshi da tutar Najeriya a kasar Faransa.
Bidiyon jirgin ruwan ya rika jawo sosai a shafukan sada zumunta inda aka rika bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai.
Babban dalilin hakan shine a baya, shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayyana aniyar sayen jirgin ruwa,saidao da suka ta yi yawa ya fasa.
Ganin wannan bidiyon yasa da yawa suka fara tunanin kodai Shugaban kasar har ya sayi jirgin ruwanne?
Saidai hadimin Shugaban kasar ta fannin kafafen yada labarai, Otega Ogra ya bayyana cewa, ba gaskiya bane labaran da ake yadawa cewa jirgin ruwan mallakin gwamnatin Najeriya ne.
Ya bukaci a yi watsi da wannan jita-jita.