
Rahotanni sun bayyana cewa, dansandan Najeriya me mukamin ASP ya kashe kansa a jihar Naija.
Dansandan me suna shafi’u Bawa na tare da runduna ta 61 ce dake Kontagora a jihar Naija kuma wata majiya ta bayyanawa jaridar Daily Trust cewa ya kashe kansa ne ranar Asabar da yamma.
An tarar gawarsa na reto ne a dakinsa da ya sagale kansa a jikin silin.
Rahotanni sunce mahaifinsa, Mallam Usman Bawa ne ya fara kai rahoton mutuwar dan nasa a ofishin ‘yansanda dake Kontagora.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an baiwa danginsa gawar inda kuma aka fara bincike akan lamarin.