Jami’an tsaro sun kashe masu garkuwa da mutane 3 a karamar hukumar Kauru dake jihar.
Jami’an tsaron sun kai samamene ranar Talata inda suka tashi wata maboyar masu garkuwa da mutanen.
Sun kuma jikkata wasu daga cikin bata garin inda suka tsere da raunuka a jikinsu.
An kubutar da mutane 25 da suka yi garkuwa dasu.