
Wata mata me dafa Kek, ta hadawa Aliko Dangote kek dan murnar zagayowar ranar Haihuwarsa.
Dangote dai ya cika shekaru 68 inda mutane ciki hadda Shugaban kasar Najeriya suka tayashi murna.
Matar ta nuna irin Kek din da ta shiryawa Aliko Dangote wanda ya hada dana motoci dana matatar mansa da sauransu.
Mutane da yawa sun yi mamakin ganin Kek din.
Aliko Dangote dai shine na farko da yafi kowa Kudi a Afrika.