Wasu mata a kasar Rasha sun lakadawa wani mutum da yaki yin lalata dasu dukan kawo wuka har ya mutu.
An dai kama matan bayan faruwar lamarin.
Matan su biyu ne inda daya sunanta Martha me shekaru 37 sai kuma Rosa me shekaru 29.
Rahoton yace suna rawa ne tare da Alexandra me shekaru 63.
Rahoton yace sun nannaushi mutumin saboda yaki yayi lalata dasu. Bayan da suka kasheshi sai suka boye gawar a cikin wani rami.
Saidai an gano gawar mutumin kuma an kama matan inda aka gurfanar dasu a gaban kuliya.