Friday, January 16
Shadow

Hotuna: Yanda shugaba Tinubu ya dawo daga kasar Brazil

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo daga Kasar Brazil inda ya halarci taron kungiyar kasashen BRICS.

Manyan jami’an Gwamnati ne suka karbeshi a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya tabbatar da dawowar shugaban kasar.

Yace daga cikin wadanda suka karbi shugaban kasar a filin jirgi akwai ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu, Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, jigo a jam’iyyar APC, Ibrahim Masari, da tsohon gwamna jihar Sokoto, Aliyu Wamakko.

Kamin kasar Brazil, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara ziyartar kasr Saint Lucia ne.

Karanta Wannan  Hadiza Gabon ta sabunta dakin da take Hira da mutane inda ta saka hotunan manyan jarumai saidai Rashin ganin Hoton Adam A. Zango ya jawo cece-kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *