Rahotanni sun bayyana cewa, an kira wasu matasa a Babban birnin tarayya,Abuja wani taro inda aka raba musu kudade Naira 1,500 dan kada su fito zanga-zanga.
Daya daga cikin matasan da aka kira wannan taron ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
Yace “NIGERIA DAI BAZATA GYARU BA!
Ɗazu wasu matasa Wai sune shuwagabannin matasan Arewa suka gayyacen taro a royal continental, zone 4, Abuja aka bamu 1500 for each akace Wai an janye zanga zanga”
Ya kuma kara da cewa “Bamukai 200 bafa a gurin meeting din Wai wakilan Arewa, Kai Nigeria sai Allah”
Lamarin Zanga-zanga dai ya tayarwa da gwamnati da sauran masu fada a ji ciki hadda malamai hankali a kasarnan inda suke ta kokarin ganin yanda za’a dakile shirin na yin zanga-zangar.