
An gano yanda wasu da ake zargin matsafane ke kwakule kaburbura bayan a binne a jihar Borno inda suke sace sassan jikin gawargwakin
Lamari na kwanannan da aka gano shine wanda ya faru a makabartar Ramon Yashi dake Bayan Kwatas a cikin Birnin Maiduguri.
An ga sabon kabari da aka binne amma an kwakuleshi an dauke gawar dake ciki, mazauna unguwar sun fara fargabar cewa da wuya idan babu matsafa ne suka aikata hakan ba.
Wani shaida ya bayyanawa majiyarmu cewa, sun hango gawa na yawo akan ruwa, kuma sun je bakabarta suka iske an tone kabari babu gawar a ciki.
Lamarin ya saka tashin hankali da fargaba a tsakanin mutanen dake zaune a kusa da makabartar inda suke kiran jami’an tsaro da gwamnatin jihar ta kai musu dauki.