
Sojoji a jihar Taraba sun kubutar da wani jami’in hukumar NDLEA da wasu 5 da aka yi garkuwa dasu.
Lamarin ya farune ranar 27 ga watan Afrilu a kan hanyar dake tsakanin Wukari–Kente a jihar ta Taraba.
Sojojin sun ce wani shugaban matasa me suna Samuek ne ya kira ya sanar da cewa ya ga mota Hulix a daji ba kowa a ciki.
Ko da sojoji suka je gurin motar ba kowa inda daga nan ne suka bazama neman mutanen cikin motar.
An kubutar da su duka, saidai Rahoton yace da kansu ne suka tsere cikin daji bayan ‘yan Bindigar sun harbesu da Bindigar farauta.
Sojoji sun gyara musu tayar motarsu data lalace sannan aka rakasu kan hanya suka ci gaba da tafiyarsu.