
Hukumar Alhazai ta Ƙasa a Najeriya ta sanar da kammala shirye-shirye domin soma jigilar maniyyata aikin Hajjin bana zuwa kasar Saudiyya ranar 9 ga watan Mayu.
Hukumar ta Nahcon ta sanar da hakan ne bayan wata ganawa da shugabanta da wakilan majalisar gudanarwa suka yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban kasar ne ya gayyaci shugaban hukumar Farfesa Abdullah Saleh Usman da wakilan sashen gudanarwa zuwa ganawar a ofishinsa domin sanar da shi inda aka kwana game da shirye-shiryen aikin hajjin.
“Mun yi masa bayani game da shirye-shiryenmu a Makkah da Madina da Arafa kuma ya gamsu, har ma ya ba mu umarnin yadda za mu haɗa kanmu mu yi aikin har zuwa ƙarshensa,” kamar yadda Farfesa Saleh ya shaida wa BBC.
Kazalika, shugaban ya ce suna sa ran kammala aikin kwashe maniyyatan a ranar 24 ga watan Mayu.
Jigilar ɗauka da mayar da alhazai na yawan zuwa da matsaloli a Najeriya kusan duk shekara, abin da hukumomi ke cewa suna aiki tuƙuru domin guje mata.
Hukumomi sun ce mutum 43,000 ne za su je babbar ibadar ta Musulmai daga Najeriya a wannan shekara. A bara mutum kusan 95,000 ne suka yi ibadar.
“A shekarar da ta wuce muna da alhazai 95,000, kamfunnan jigila uku muka bai wa aiki. Yanzu da muke da alhazai 43,000 mun ɗauki kamfunna huɗu. To ina maganar ƙarancin jirage a nan?,” in ji farfesan.
A cikin tawagar hukumar, akwai wakilan fannoni daban-daban kamar na zirga-zirgar jiragen sama, da na shige da fice, da sauransu, wadanda ga alama su ma sun yi wa mataimakin shugaban bayani.
DCJ M.T. Umar, shi ne ke wakiltar hukumar shige da fice ta Najeriya a Nahcon, kuma ya ce sun kammala babban aikinsu a shirin aikin Hajjin na bana – wato yi wa maniyyatan fasfon tafiya.
“Babu maniyyacin da ya nuna aniyar zuwa aikin Hajji da bai samu fasfo ba zuwa yanzu, kuma ba mu da wata matsalar rashin kayan aiki a kowace cibiya a ƙasa baki ɗaya,” a cewarsa.
A ‘yan makonnin nan ne ‘yan majalisar gudanarwar hukumar suka rubuta wa Kashim Shettima koke, suna zargin shugaban Nahcon Farfesa Abdullah Saleh da mayar da su saniyar ware wajen gudanar da lamurran hukumar, zargin da shugaban ya musanta.
Wakilin BBC da ya halarci ganawar, Haruna Shehu Tangaza, ya ce da alama taron wata hanya da mataimakin shugaban ƙasar zai iya sanin ko an ɗinke barakar kamar yadda ya umarta a watan jiya.