
Hukumar kula da babban birnin Tarayya, Abuja, FCTA ta kwace filin hedikwatar jam’iyyar PDP dake Abuja.
A takardar kwace filin da hutudole ya karanta, hukumar FCTA tace PDP taki biyan harajin da ya kamata ta biya na kan filin kusan tsawon shekaru 20 da suka gabata kenan.
Kuma tun shekarar 2023 ake ta tunatar da PDP game da biyan harajin amma ta yi kunnen uwar shegu.
Dan hakane yanzu an kwace filin ya zama mallakin hukumar FCTA din dake Abuja.