
Hukumar EFCC Ta Miƙa Rukunin Gidajen Alfarma 750 Da Ta Kwace A Hannun Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefele Ga Ma’aikatar Gidaje Da Raya Birane Domin Sayar Da Su Ga Ƴan Najeriya, Yau Talata
EFCC ta danƙa gidaje 753 da ta ƙwace a hannun Emefiele ga gwamnatin taraiya
Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta mika wani gidaje 753 da ke da alaka da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN ga ma’aikatar gidaje da raya birane ta taraiya.
Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ne ya mika takardun rukunin gidajen ga Ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa a yau Talata.
Rukunin gidajen, wanda ba a kammala ginin su ba, na cikin gundumar Lokogoma na babban birnin tarayya Abuja.
A wata sanarwa da Dangiwa ya fitar ta ce shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kammala gidajen da aka kwato tare da sayarwa wa al’ummar Najeriya ta hanyar gaskiya da rikon amana.
Dangiwa ya ce ma’aikatar za ta tabbatar da cewa an kammala duk wasu gine-ginen da aka tsare yin su domin tabbatar da cewa gidajen sun kammala kuma sun dace da matsuguni na ka’ida.
A Ganin Ku Farashin Su Za Su Kai Naira Kuma Su Wa Za Su Saye Su?
Daga Jamilu Dabawa