
Hukumar jirgin kasa ta Najeriya, The Nigerian Railway Corporation ta sanar da rage farashin Tikitin jirgin da kaso 50 saboda bukukuwan karshen shekara.
Hukumar tace ragin zai fara aiki ne a yau, Talata.
A ranar 25 ga watan Disamba ne za’a yi bikin Kirsimeti sannan akwai bikin karshen shekara na 1 ga watan Janairu wanda duka Gwamnati ta bayar da hutu.