
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa, NATCA ta bayyana cewa aiki yawa ma’aikatanta yawa saboda karancin ma’aikata da hukumar ke fama dashi.
Hukumar tace akwai bukatar a dauki ma’aikata musamman dan saukaka aikin hukumar.
Shugaban kungiyar ma’aikatan hukumar, Mr Amos Edino ne ya bayyana haka inda yace aiki yanawa ma’aikatansu yawa wanda hakan yake sa su kasa kammala aikin yanda ya kamata.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a filin jirgi na Murtala Muhammad dake Legas.
Yace a ka’ida, ma’aikatansu aikin awanni 2 kawai ya kamata su rika yi suna tashi kamin wani yazo ya karbeka, yace amma yanzu ma’aikatansu har aikin awanni 4 suna yi.
Yace makarantar horas da matuka jirgin sama dake Zaria, NCAT dake da alhakin horas da irin wadannan ma’aikata itama tana fama da karancinsu.
Sannan yayi kira ga gwamnati data inganta albashinsu yayi daidai dana sauran kasashen Duniya.