
Hukumar ‘yansanda a jihar Legas sun fitar da sanarwa game da zanga-zangar da ake shirin yi gobe a fadin Najeriya.
Hukumar ‘yansandan ta gargadi masu zanga-zangar kada wajan gudanar da zanga-zangar su rika hayewa ‘yansanda suna cin zarafinsu.
Kungiyar TIB da wasu kungiyoyin ne suka shirya wannan zanga-zangar inda suka ce suna so ne a soke dokar saka ido a kafafen sada zumunta da yanar gizo da kuma janye dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
Saidai a sanarwar da hukumar ‘yansandan jihar Legas din ta fitar ta bakin kakakinta wadda DCP Tijani O. Fatai ya sakawa hannu, yace sun lura da cewa, ana amfani da wahalar da ake ciki wajan jawo mutane su fito zanga-zangar.
Ya bayyana cewa, zasu saka mutanensu a gurare daban-daban na fadin jihar dan tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar.