
Hukumar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Delta sun gargadi matasa da cewa, akwai tarar Naira Dubu 50 ga duk wanda aka kama da shigar banza.
Hukumar ‘yansandan jihar ta wallafa sakonne a shafinta na X ranar Asabar inda tace hakan kokari ne na wayar da kan mutane game da dokokin jihar.
Hukumar ‘yansandan jihar tace ta yi hakanne dan wasu zasu ce basu dan da wannan doka ba to dan a kiyaye tace zata rika wallafa irin wadannan dokoki akai-akai.