
Kungiyar ‘yan Kasuwar man fetur na Najeriya, PETROA sun yi gargadin cewa, idan Matatar Man fetur din Dangote ta ci gaba da rage farashin man fetur din ta, zasu iya karyewa.
Kungiyar ta bayyana hakane ta bakin shugabanta, Dr. Billy Harry.
Yace ana kokarine a hanasu shigo da man fetur daga kasashe waje shiyasa ake wannan ragin farashin.
Hakan na zuwane bayan da matatar man fetur din Dangote ta rage faashin man fetur din ta daga Naira N835 akan kowace lita zuwa Naira N825 akan kowace lita.
Dr. Billy Harry yace tun safe suke ta taro dan gano hanyar da zasu magance wannan matsala baya da suka samu labarin age farashin man.