
Kakakin majalisar Dattijai ya gargadi bangaren zartaswa akan su daina sukar shawarar da majalisar ke bayarwa kan yanda za’a magance matsalar tsaron kasarnan.
Majalisar Dattijai dai ta bayar da shawarar a yi taron karawa juna sani na kwanaki 2 dan samo hanyar da za’a magance matsalar tsaron Najeriya.
Saidai Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa ba ta irin hakane za’a kawo karshen matsalar tsaro ba inda yace kwamandojin sojoji ne ke bayar da odar yanda za’a kai hari da magance matsalar tsaro ba taron farar hula ba.
Wannan magana dai bata yiwa majalisar Dattijai dadi ba inda kakakin majalisar Godswill Akpabio yace ministan yayi hankali kada ya kawo rashin jituwa tsakanin majalisar da bangaren zartaswa.
Sannan yace idan ya zamana bangaren zartaswa suna sukar shawarar da majalisar ta bayar to matsalar tsaro ba raguwa zata yi ba saidai ma ta kara karuwa ta kazance.
Yace ko da bangaren zartaswar basu yadda da abinda majalisar ta fada ba, kamata yayi su aika musu da sako ba tare da fitowa Duniya su bayyana ba.
Hakanan shima Shugaban majalisar, Opeyemi Bamidele yace mutanene suka zabesu dan su wakilcesu a gwamnatance kuma zasu yi dukkan mai yiyuwa wajan ganin sun magance matsalar tsaron kasarnan, yace irin wannan kalamai zasu iya kawo rashin jituwa da hadin kai tsakanin majalisar da bangaren zartaswa.