
Jam’iyyar ADC ta gargadi Peter Obi da cewa kada ya sake ya barta.
Hakan na zuwane bayan da wani shugaban magoya bayan Peter Obi me suna Yunusa Tanko yace Peter Obi zai yi takarar shugaban kasa ko da jam’iyyar ADC ko babu ita.
Hakanan ya jawo hankalin Jam’iyyar ADC din data tsayar da dan kudu takarar shugaban kasa maimakon dan Arewa.
Saidai a martanin shugaban matasa na jam’iyyar ADC, Comrade Abayomi Bello yace idan dai wannan magana daga bakin Peter Obi ta fito to lallai yana barin jam’iyyar siyasarsa ta zo karshe.
Yace maimakon barin ADC idan bai samu takarar shugaban kasa ba, kamata yayi Peter Obi ya tsaya a gina jam’iyyar dashi.