
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, idan aka dage a Afrika, cikin shekaru 5 za’a iya mayar da nahiyar Aljannar Duniya.
Ya bayyana hakane a wajan wata hira da aka yi dashi.
Dangote ya bayyana cewa, babbar matsalarmu a Afrika shine satar kudi da ake ana kaiwa kasashen ketare.
Yace babu inda ba’a rashawa da cin hanci, yace amma matsalar ta Africa shine, maimakon idan an sata a zuba jari da kudin a Afrika, sai a mayar dasu zuwa kasashen waje.
Dangote yace ba wai yana karfafa satar kudin Gwamnati bane amma abinda yake cewa, shine a daina kai kudaden kasashen waje.