Friday, December 5
Shadow

Idan na ci amanar Tinubu na zama shedan kuma Allah sai ya azabtar dani>> Ministan Ayyuka David Umahi

Ministan ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa saboda yaddar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya masa, idan ya ci amanarsa ya zama shedan.

Umahi yace Tinubu ya bashi aikin sayo kayan wani aiki da za’a yi da kudin suka kai Naira Tiriliyan 1.6, yace amma abin mamaki Tinubun bai taba kiransa ya ji ko ya ake ciki ba.

Umahi yace na kowane zai iya maka wannan abin ba dan haka shi ya fada har a gaban Tinubu cewa, daga Allah sai shi a wadanda yake girmamawa dan yafi iyalansa.

Umahi ya bayyana hakane a Abakaliki yayin ganawa da manema labarai.

Karanta Wannan  A karshe dai da suka ga ba zasu iya hanata ba, Yanzu kasar Amurka tace ta yadda kasar Iran ta ci gaba da kokarin mallakar makamin kare dangi amma bisa sharudin ta daina gaggawa wajan inganta Makamin Uraniyum, ta rika yi a hankali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *