
Wani matashi me suna Iliyasu Muhammad dake zaune a Dantata Village a babban barnin tarayya Abuja ya kashe abokinsa ta hanyar datsashi da adda.
Iiliyasu ya gayyaci abokinsa, Saifullahi Muhammad gidansa dan cin abinci inda a yayin da Saifullahi ke cin abincin ne, Iliyasu ya hau kansa da sara.
Kakakin ‘yansandan Birnin Tarayya, Abuja, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace an kirasu ranar February 13, 2025 da misalin karfe 1:30 na rana inda aka sanar dasu abinda ya faru.
Tace da suka je sun iske Saifullahi cikin jini inda suka kwasheshi zuwa Asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.
Tace an kama Iliyasu kuma ya amsa laifinsa.
Ta kara da cewa, da bincike yayi tsanani, sun gano Iliyasu na tare da wasu gungun mugayene dake yiwa masu mashina kwace a Abuja inda suke aikin tare da wani me suna Hassan wanda tuni ya tsere.
Ta kara da cewa sun kuma gano an taba daure Iliyasu a gidan yari.
Tace suna kan kokarin kama sauran abokan aikin Iliyasu dan tabbatar an hukuntasu.