
Wata ƴar Najeriya da ke zaune a Amurka, Gimbiya Adenubi Olagbegi-Apampa, wacce mahaifinta ke da mata 39 da ‘ya’ya 147, ta ce tana alfahari da fitowa daga irin wannan babban gida.
Ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a wajen bikin bada kyautar wani gini mai suna Gimbiya Nubi Plaza Seliat na miliyoyin naira da ke Estate Lagelu, Ibadan.
A cewarta, idan har ta samu dama ta sake zuwa, za ta ji dadin zama a wannan gidan yawan.
Sabanin cewa irin wannan gidan yawan ba a raba shi da rikici, ta bayyana cewa duk ƴaƴan gidan nasu su na zaune lafiya da juna.
Ta kuma bukaci ƴan Najeriya mazauna kasashen waje da kada su yi amfani da matsalar rashin tsaro su kaurace wa kasarsu.
Ta lura da cewa rashin tsaro da cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare a Najeriya ba iya nan kasar bane kawai, inda ta kara da cewa ƴan Najeriya ba su san cewa Amurka ma a matsayinta na kasa mai cike da ci gaba na fama da wadannan matsaloli ba.