
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana xewa kamfaninsa na yin takin zamani suna tsammanin zai rika samar da kudin shiga da suka kai dala Miliyan $20 kullun.
Yace kuma suna tsammanin kamfanin zai samar da kudaden shigar da suka kai dala Biliyan $70.
Ya bayyana hakane yayin ziyarar da shuwagabannin hukumar hadahadar kasuwancin hannun jari suka kai masa matatar man sa dake Legas.
Sun bashi tabbacin taimakawa dan saka kamfanin nasa na yin takin zamani a kasuwar saye da sayarwar hannun jari.