Sunday, March 16
Shadow

Ina da kwararan shaidu cewa mijin ki mijin ki ɗan neman mata ne – Sanata Natasha ga matar Akpabio

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bukaci Ekaette Akpabio, matar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da ta send tsoma baki a batun zargin da ta ke yi wa mijin na ta na neman mata.

A wata hira da aka yi da ita a tashar Arise a ranar Juma’a, Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta bayyana cewa Akpabio ya yi mata tayin lalata a ofishinsa da kuma gidansa da ke Akwa Ibom.

Hakan ne ya sanya matar Shugaban Majalisar Dattawan, Ekaette, ta mayar da martani inda ta ce mijinta mutum ne mai kamun kai, kuma ta ce ikirarin sanatar “karya ne.”

Ekaette ta kuma shigar da kara a kotu kan take hakki ta da ɓata suna da Akpoti-Uduaghan ke yi.

Karanta Wannan  An kama magidanci da ya Kkàshè matarsa

A cikin wata wasika mai kwanan wata 1 ga Maris, da aka aikawa matar Shugaban Majalisar, sanatar, ta hannun lauyanta, Victor Giwa, ta ce ba ta da sha’awar saka Ekaette cikin wannan lamari mai ban takaici.

Sanatar ta shawarci Ekaette da ta kula kuma ta bar mijinta ya kare kansa daga wadannan zarge-zarge.

“Wacce muke karewa tana da hujjoji masu karfi da za su tabbatar da zarge-zargen da ta yi. Don haka muna ba da shawarar ki bar wa Shugaban Majalisar damar kare kansa, domin ki kare da na iyalanki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *