
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, idan aka binciki Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da matarsa akan kudaden hukumar NDDC ba’a samesu da laifi ba, zai sauka daga Ministan Abuja.
Wike ya roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya saki rahotan binciken hukumar wadda ta raya yankin Naija Deltace.
Wike ya fadi hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV inda yake mayar da martani kan zargin da Amaechi ya masa cewa, shi dan rashawa ne.
Wike yace NDDC ta rika baiwa matar Amaechi Naira Biliyan 4 da sunan zata baiwa mata horo duk wata.
Yace dan haka yake rokon shugaba Tinubu ya taimaki ‘yan Najeriya tmya wallafa sakamakon binciken da aka gudanar.
Wike yace ko a makaranta Amaechi dakiki ne.