Friday, December 26
Shadow

Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa cikin matsala – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana farin ciki da halin rikici da jam’iyyun adawa da dama na ƙasar ke ciki.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin jawabin da ya yi na ranar tunawa da dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, yau Alhamis.

“Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa a tagayyare,” kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya.

Tinubu ya ce “ba zan ce ina so na ga kun gyaru ba, ina ma jin dadin ganin ku a haka.

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ke ci gaba da karɓar ƴan siyasa masu sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa cikinta.

Karanta Wannan  Wani Mai Suna Ãbdüllàhí Beguwa, Wato Daya Daga Cikin Matasan Dake Zugawa A Ýi Źànga-Źàñga Ya Hada Kayansa Ya Baŕ Ķàśaŕ, A Yayin Da Ake Gaf Da Fara Zàñga-Zangar

Tinubu ya ce jam’iyyar APC ba za ta hana kowa shiga cikinta ba domin yin hakan tauye hakkin al’umma ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *