
Tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana Buhari a matsayin wanda yawa ‘yan Najeriya yaudarar da ba’a taba musu irin ta ba.
Ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi.
Yace ya yiwa Buhari yakin neman zabe a baya kuma dashi aka kafa jam’iyyar APC amma maganar gaskiya Buhari ya boye bakar aniyarsa ce a zuciya inda ya rika nuna yana tare da talakawa, sai daya hau mulki ya fito da ainahin kalarsa.
Yace amma ba zai yi magana sosai akan lamarin ba ‘yan Najeriya ne zasuwa kansu alkalanci game da wanene Buhari.
Ya kara da cewa Buhari kamata yayi ya koma ya ci gaba da neman gafarar Allah biyo bayan zaluncin da yawa mutane.