
Sanata Ned Nwoko ya bayyana cewa, yana tausayawa maza masu mace daya.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Channels TV inda yace mace daya kamar mutum na tsayene akan kafa daya, da ta samu matsala shikenan.
Yace amma idan mutum na da mata da yawa, zai fi samun nutsuwa.
Game da maganar matarsa, Regina Daniels yace ba gaskiya bane da ake yada cewa ya ci zarafinta ta hanyar duka, yace shi yana ganin girman mata.