
Sanata Garba MaiDoki daga jihar Kebbi ya bayyana cewa suna da masaniya kan inda ‘yan Bindiga suka boye ‘yan mata ‘yan makaranta da suka sace.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Channels TV inda yace ba’a fita da ‘yan matan daga yankin Kebbi ta kudu ba.
Ya kuma bayar da tabbacin nan da kwanaki 1 zuwa 2 za’a dawo da ‘yan matan.
‘Yan mata ‘yan makaranta su 25 ne dai aka sace daga Maga jihar Kebbi.