INEC Na Duba Yiwuwar Bai Wa ’Yan Najeriya Damar Kada Kuri’a Ba Tare da Katin Zabe (PVC) Ba.

Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) tana nazarin sabon tsari da zai bai wa ’yan ƙasa damar kada kuri’a ba tare da katin zabe na dindindin (PVC) ba a babban zaɓen 2027.
A cewar hukumar, sabon tsarin zai dogara ne da amfani da fasahar zamani kamar BVAS (Bimodal Voter Accreditation System) da kuma takardun tantancewa da za a iya saukewa daga shafin INEC. Wannan zai rage wahalhalu, rage kashe kuɗi, da hana saye da satar katin zabe.
Sai dai, kafin wannan tsari ya fara aiki, ana buƙatar gyara dokar zabe wanda ya shafi Majalisar Dokoki domin samun doka da izinin amfani da tsarin.
Wannan mataki na INEC na nuni da kokarinta wajen saukaka tsarin zabe da kara amfani da fasaha don tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓuɓɓuka.