Ga wasu daga cikin ingantattun sunayen Musulunci tare da ma’anoninsu:
Sunayen Maza:
- Muhammad: Sunan Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “wanda ake yawan yabawa”.
- Ahmad: Wata ma’ana ta Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “wanda aka fi yabawa”.
- Ali: Sunan Sayyidina Ali, yana nufin “mai daraja” ko “mai girma”.
- Hassan: Sunan jikan Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “mai kyau”.
- Hussain: Sunan jikan Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “mai kyau karami”.
- Abdullah: Yana nufin “bawan Allah”.
- Umar: Sunan Sahabin Annabi, yana nufin “mai tsawon rai” ko “rayuwa”.
- Usman: Sunan Sahabin Annabi, yana nufin “mai kariya” ko “mai juriya”.
- Yusuf: Sunan Annabi Yusuf (AS), yana nufin “Allah ya ƙara”.
Sunayen Mata:
- Fatima: Sunan ‘yar Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “me tsarki”.
- Aisha: Sunan matar Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “rayuwa” ko me nasara.
- Khadija: Sunan matar farko ta Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “me gaskiya”.
- Zainab: Sunan ‘yar Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “kyakkyawan furanni”.
- Maryam: Sunan mahaifiyar Annabi Isa (AS), yana nufin “wadda ake so” ko “mai addu’a”.
- Asiya: Sunan matar Fir’auna mai imani, yana nufin “Me kwarin gwiwa”.
- Hafsa: Sunan matar Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “ta macen zaki”.
- Ruqayyah: Sunan ‘yar Annabi Muhammad (SAW), yana nufin “wadda Allah ke so”.
- Sumayya: Sunan sahabiyar Annabi, yana nufin “Ta musamman” ko “Madaukakiya”.
Wadannan sunayen suna da tarihi mai zurfi a Musulunci, kuma suna da ma’anoni masu kyau da dacewa ga masu suna.