Friday, December 5
Shadow

INNA LILAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Abokiñ Wasañ Kwallonsà Ya Càķa Màsà Aĺmàkàshì Ya Rasu A Kano

Wani mummùñan lamari ya faru a filin wasan kwallo na Shagari Quarters dake cikin garin Kano, inda wasu bata-gari suka kàśhe wani matashi mai suna Baba, ɗan asalin Jos, a cikin filin wasa.

Yadda lamarin ya auku shine, wanda aka kaśhe, Baba, yana cikin wasa ne lokacin da ya ci kwallo, sai jikinsa ya bige wani yaro da ake kira Bello (Belloty). Alkalin wasa bai busa ketar ba, wanda hakan bai yi wa Belloty dadi ba. Bayan an kammala wasan, Belloty ya bi Baba da zargin me ya sa ya bige shi, hatsaniya ta barke tsakaninsu.

Abokin Belloty, wanda ake kira Hafizu (wanda aka fi sani da “Mata”), ya miƙa masa almàķashi, inda Belloty ya caka wa Baba cìkin źùçiya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa a nan take.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yanda wata mata ke rawar Fitsara a coci da yawa sun ce ba ibada ta ce yi ba...

Belloty (wanda ya caka almakashi) da Hafizu “Mata” (wanda ya mika almakashiñ) dukkansù sun gudu daga wajen, inda ake neman su ruwa a jallo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *