INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Miji Da Matarsa Sun Ŕàsu Sakamakoñ Gobara Ana Gobe Sallah.

Sadiq da Khadija sun kasance mata da miji wadanda Allah Ya yi musu rasuwa sakamakon gobaraŕ wutàŕ nepa da ta tashi a dakinsu’ a garin Alkaleri dake jihar Bauchi da asubahin ranar Alhamis din da ta gabata.
Marigayin wanda ya zo gida yin bikin sallah, suna cikin bacci wajen karfe 3 zuwa 4 na asuba wutar nepa ta kama dakinsu, inda gobarar ta faro daga falo daga bisani ta shigo har cikin uwar daki. Duk kokarin da suka yi na neman ceton ransu abin ya ci tura, inda daga karshe suka shige bandaki ko abun zai zo musu da sauki.
Wani abun tausayawa shine, a lokacin da aka same su ba rai an ga yana rike da ita ya kare ta saboda kada wani abu ya same ta har ma wuta ya dan taba shi ta bayansa saboda kare ta da ya yi, kamar yadda Rariya ta samu labari.
Da aka kawo musu dauki bayan an kashè wutar, ba a yi tsammanin suna ciki ba saida mahaifiyarsa ta zo ta ce Sadiq da matarsa suna ciki, inda bayan an
duba bandakin sai aka samu sun rasu, kuma wutaŕ ba ta kama bandakin ba, iya zallar hayaki ne da kuma rashin iska da turirin wutar ya sa suka rasa ransu.
Daga Adamu Mohammed Damina