
“Daga Yau Na Bar Dariqa Kuma Ina Neman Afuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi da Iyalansa” Umar Ambato
“Nabar Darika daga yau ina kuma neman afuwar Dr Idris Dutsen tanshi da iyalansa da masoyansa musamman wadanda su ke a wannan kafa ta Facebook, sakamakon abin da ya faru dani a cikin baccin da na yi daren jiya, nayi mafalki Dr Idris Dutsen Tanshi yana cikin aljanna, mu yan Dariku an tara mu za’a kai mu wutar Jahannama”.
“Tunda na tashi daga bacci bana jin karfin jikina, hankalina ya tashi sosai”
“Dan Allah ku taimaka ku watsa labarin nan ga yan dariku su ji su gani ma idonsu ko za’a samu mai rabo yabar darika kamar yadda na bari”.