
Ministan Matasa,Ayodele Olawande yace gyaran da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zaiwa Najeriya zai sa ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje su so dawowa gida.
Yace duka abinda shugaban kasa ke yi yana yi dan gobene, yace nan gaba kadan Najeriya zata gyaru sosai da zata rika baiwa ‘yan Najeriya dake kasashen waje sha’awa su dawo gida.
Yace yanzu gwamnati na jawo matasa a jiki dan su san ana yi dasu.