Saturday, December 13
Shadow

Isra’ila ta lalata asibiti na ƙarshe a arewacin Gaza – WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sojojin Isra’ila sun lalata babbar cibiyar lafiya ta ƙarshe da ta rage a arewacin Gaza.

WHO ta ce rahotanni sun bayyana cewa an ƙona wasu muhimman sassa da aka lalata a harin da aka kai ranar Juma’a a asibitin Kamal Adwan.

Hukumar ta kuma nuna matuƙar damuwa game da lafiyar majinyatan da aka tilasta musu barin asibitin.

Isra’ila dai ta ce Hamas na amfani da asibitin ne a matsayin cibiyar ba da umarni – amma ba ta gabatar da wasu hujjojin da ke gaskanta hakan ba.

Karanta Wannan  Inason gina Masallaci da kudaden da nike samu daga wakokin da nake yi, Kuma nasa ba zaku ce ba zaku yi Sallah a masallacin ba>>Inji Soja Boy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *