
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma me ikirarin fafutukar ‘yancin dan Adam, Omoyele Sowore ya bayyana cewa Gwamnonin jihohin Bauchi, da Katsina, da Kano, da Kebbi da suka bayar da hutun makaranta na Azumin watan Ramadana Jahilaine kuma sakarkarune.
Yace Makka da ake zuwa yin hajji basu kulle makarantun su saboda Azumin watan Ramadana ba wanda hakan yake nuna cewa su wadannan gwamnoni sun jahilci addinin.
Yace idan ya zama shugaban kasa, ba zai bari wani gwamna yayi irin wannan abin ba.
Sowore ya kara da cewa, cikin makarantun da aka kulle hadda na islamiya inda yace idan makarantun Islamiya na kulle ta yaya yara zasu koyi Qur’ani?