
Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta saka ranar Alhamis 24 ga watan Afrilu a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar, ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da kumar ta ce muhimman matakan da ta ɗauka da kuma dauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin.
Dr Fabian Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar – wadda ke ɗauke da muhimman bayanai dangane da jarrabawar.
Ya ƙara da cewa akwai bayanin wuri da lokacin mutum zai zana jarrabawar da sauran muhimman bayanai game da yadda tsarin zaman ɗakin jarrabawar zai kasance duka a jikin katin.
Dubban ɗaliban Najeriya ne ke rubuta jarrabawar JAMB a kowace shekara, domin samun damar shiga makaratun gaba da sakandire.