DA ƊUMIƊUMINSA: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam’iyyar PDP A Abuja.

Daga Muhammad Kwairi Waziri
A safiyar yau Litinin, an jibge jami’an tsaro a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja, gabanin babban taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) da aka shirya gudanarwa a yau.
Jami’an ‘yan sanda, DSS da Civil Defence sun mamaye ko’ina a harabar ofishin jam’iyyar domin tabbatar da tsaro yayin taron, wanda ake ganin zai yanke muhimmiyar shawara kan makomar jam’iyyar da shugabancinta.
Wata majiya daga cikin jam’iyyar ta bayyana cewa ana sa ran tattaunawa mai zafi kan shugabancin jam’iyyar na ƙasa, inda ake hasashen sauyin wasu muƙamai ko sabbin shawarwari game da tsarin PDP na gaba.
Ana sa ran dattawan jam’iyyar, gwamnoni da wakilan PDP daga jihohi daban-daban za su halarci taron. Wasu daga cikin batutuwan da za a tattauna sun haɗa da: rikicin cikin gida, zabukan da ke tafe, da makomar jam’iyyar a 2027.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da sabani a cikin jam’iyyar kan wasu matsalolin shugabanci da sauye-sauyen da ake muradin yi.
Taron NEC na yau zai iya zama wata sabuwar dama ko barazana ga jam’iyyar PDP yayin da take shirin sake daidaita kanta gabanin babban zaben 2027.