Friday, December 5
Shadow

Jam’iyyar Adawa ta kayar da shugaban kasa me ci a kasar Malawi, kuma ya amince da shan kaye

Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya amince da shan kaye bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Laraba.

Ɗantakarar adawa Arthur Peter Mutharika na jam’iyyar Democratic Progressive Party ne ya lashe zaɓen.

“Sakamakon zaɓen ya nuna ƙarara cewa babban abokin adawata Farfesa Mutharika ya samu ƙuri’u mafiya yawa. Saboda haka, na kira Mutharika domin taya shi murna kan nasarar da ya samu,” in ji shugaban cikin wani jawabi da ya yi ‘yan mintuna da suka wuce.

Ana sa ran hukumar zaɓe Malawi Electoral Commission za ta sanar da nasarar tasa.

Karanta Wannan  Ni ne gatan 'yan Najeriya, Duk wani da zai zo ya ce muku zau kayar dani zabe a 2027 kada ku saurareshi>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *