
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta gayyaci tsaffin Gwamnoni 3 na jam’iyyar ADC.
Hakan ya saka rudani a jam’iyyar ta ADC inda sukw zargin kokarin murkushe su ne yasa EFCC ta fara bincken membobin jam’iyyar.
Tuni dai EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal inda take tuhumarsa bisa cire wasu kudi da suka kai Naira Biliyan 189 lokacin yana gwamnan Sokoto.
Me magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa, wannan abu ana kokarin ganin an tursasa mutane sun bar jam’iyyar ta ADC ne.
Inda ya tabbatarwa da jaridar Punchng cewa an gayyaci tsaffin gwamnoni 3 zuwa EFCC amma yace ba zai fadi sunayensu ba.