
Ministan Sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa, Da wahala Su Peter Obi da Atiku Abubakar su wa APC kwacen mabiyan da suke dasu a Arewa.
Yace da wuya ‘yan Adawar su yi wani katabus a zaben na shekarar 2027.
Keyamo yace har yanzu APC da Tinubu suna da magoya baya sosai a Arewa wanda hakan zai sa su samu nasara a zabe me zuwa.
Keyamo yace irin Mabiyan da APC ke dashi a Arewa su Atiku ba zasu iya kai labari ba.