Friday, December 5
Shadow

Jarumin finafinan Bollywood Dharam ya ragamu gidan gaskiya

Fitaccen jarumin finafinan masana’antar Bollywood ta Indiya, Dharmendra wanda ake kira da Dharam ya rasu a birnin Mumbai na Indiya yana da shekara 89 a duniya.

Firaministan India Narendra Modi ya bayyana jajensa ga iyalan mamacin da ƴan ƙasar baki ɗaya, sannan ya bayyana rasuwar jarumin da “ƙarshen zangon jaruman sinima a Indiya.”

Dharmendra, wanda ya kasance yana bayyana da “mutum mai sauƙin kai” ya daɗe yana jan zarensa a harkar fim, inda yake nishaɗantar da miliyoyin masoyansa a duniya.

Ya yi fice da sunan Veeru saboda rawar da ya taka a fim ɗin Sholay a shekarar 1975, sannan ya fito a finafinai sama da 300 a gomman shekaru da ya yi a masana’antar.

Karanta Wannan  Karuwanci ya kaita jihar Legas>>Hadimin Shugaban kasa ya zargi matashiya 'yar Bautar kasa data soki Shugaba Tinubu

An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 1935 a ƙauyen Nasrali da ke lardin Punjab Ludhiana. Malaminsa a makaranta ne ya saka masa suna Dharam Singh Deol.

A tattaunawarsa da BBC a 2018, ya ce mahaifinsa karatu ya so ya yi, amma shi tun da farko fim yake sha’awa, wanda hakan ya sa ya fi mayar da hankali kan harkar ta nishaɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *