
Habu dan Damusa da ya rigamu gidan gaskiya ya gamu da ajalinsa ne a hannun jami’an tsaro kamar yanda rahotanni suka bayyana.
Wasu sun rika murna da mutuwarsa inda wasu kuma suka rika jimami da nema masa rahama.
Saidai sabon bayani da ya fito game dashi shine, ashe gadon daba yayi, mahaifinsa ma dan dabane, kuma shima an kasheshi ne ranar da aka haifi Habu Dan Damusa.
Hakanan ga habu shima an kasheshi kwana daya bayan da aka haifa masa diyarsa.