Monday, December 16
Shadow

Ji Ainahin dalilin da yasa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa

Rahotanni sun bayyana cewa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wucin gadi inda yace zai taci hutun sai abinda hali yayi.

Ya bayyana dalilin cewa, wani daga cikin iyalansa ne ba lafiya shiyasa ya dauki wannan mataki duk da yake bai masa dadi ba.

Saidai a binciken da jaridar Daily Nigerian ta gudanar, ta gano cewa ba haka abin yake ba.

Jaridar tace wasu na kusa da shugaban kasa ne suka fara sakawa Ajuri ido kan cewa mukaman da yake rike dasu sun masa yawa kuma sun ci karo da aikinsa na matsayin me magana da yawun shugaban kasa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Matashi da ya kammala karatun Digiri daga jami'ar Umar Musa 'Yar'Adua da sakamakon Digiri mafi daraja watau First Class na tallar Ruwa a Titin Abuja

Dan hakane suka bukaci ya zabi daya daga cikin mukaman da yake rike dasu ya ajiye sauran, jaridar tace na hannun damar shugaban kasar, sun dauka cewa zai ajiye aikin magana da yawun shugaban kasa ne amma sai ya zabi ya ci gaba da magana da yawun shugaban kasa ya ajiye sauran ayyukan da yake.

Saidai hakan bai musu dadi ba wanda hakan yasa, suka bukaci dole ya sauka daga mukamin shine yace ya hakura da aikin gaba daya amma ya fake da cewa, wani ne a cikin iyalansa ba lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *