Friday, December 5
Shadow

Ji bayani Dalla-Dalla: DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA

DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA.

Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana bayyana cewar sai dai aka hada da jami’an tsaro aka ceci Dan wasan barkwanco Ali Art-work Wanda aka fi sani da Madagwal.

Madagwal ya fada komar Yan Kwankwasiyya ne jiya Lahadi lokacin daya sake zuwa karbar darikar Kwankwasiyyar, a hannun Ubanta Injiniya Rabiu Musa, a wani taro da suka gudanar na bikin Sallah a Jihar.

Kafin Yanzu bayan ficewar sa a shekararun baya Madagwal ya koma suka da jefa kalaman batanci ga Rabiu Musa Kwankwaso da sauran Magoya bayan sa.

Haka Kuma ya sha chachchakar salon Mulkin Abba Kabir Yusuf, tare da bukatar cewar Kwankwaso ya yiwa Gwamnatin Jihar Kano kakagida shi yasa baa tabuka abun a zo a gani.

Karanta Wannan  Gwamnatin Zamfara ta mayar da dabbobi 3,000 da aka sace ga asalin masu su

Wannan ya Saka Yayan-kwankwasiyya suka kullace shi har suka dunga shan alwashi.

Ana tsaka da haka Madagwal ya zagaya, ya bayar da hakuri aka yafe masa.

To a lokacin taron su na jiya kawai sai mabiya Kwankwasiyyar suka gan shi ya zo sake jaddada bukatar cigaban tafiyar har ma aka Saka masa Jar hula.

Wannan ya fusata Magoya bayan tafiyar, Kuma duk da kashedin da aka yi musu, sai da suka farmaki Madagwal don sai da aka hada da jami’an tsaro aka fice da shi a guje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *