
Kusan za a iya cewa da wuya gari ya waye a Najeriya ba tare da ƴan siyasa daga jam’iyyun hamayya sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ba, walau dai a matakin tarayya ko kuma jihohi da ƙananan hukumomi.
Sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC da ya fi bai wa ƴan Najeriya mamaki a baya-bayan nan shi ne na ]tsohon ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa na babbar jam’iyya mai hamayya ta PDP, kuma tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Efeanyi Okowa tare da gwamnan jihar mai ci, Sheriff Oborevwori.
Bugu da ƙari, ko a wannan makon ma sai da jam’iyyar mai mulki ta karɓi sabbin masu sauya sheƙa daga jam’iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi, inda duka ƴan majalisar dattawan jihar suka koma APC.
Wannan ya janyo ƴan Najeriya ke neman sanin irin dubarun da jam’iyya mai mulkin ke bi wajen sarƙafo abokan hamayya zuwa cikinta.
Waɗanne dabaru Tinubu ke amfani da su?
Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami’a a Kano, CAS Kano da Dakta Mukhtar Bello Maisudan, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Bayero da ke Kano, sun lissafa dabaru guda huɗu da suka ce na mutum biyu ne wato shugaba Bola Tinubu da shugaban jam’iyyar ta APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
1) Alaƙa da gwamnoni da manyan ƴan siyasa
Malam Kabiru Sufi ya ce sauya sheƙar da abokan hamayya ke yi zuwa jam’iyya mai mulki ba zai rasa nasaba da yadda shugaba Tinubu ke amfani da gwamnonin jihohi na jam’iyyarsa wajen zawarcin ƴan majalisar tarayya daga jihar zuwa jam’iyyar APC.
Bugu da ƙari, ana yi wa Tinubu kallon gogaggen ɗan siyasa wanda ka iya haɗa kai da manyan ƴan siyasar jiha ko yanki domin ribato gaggan ƴan siyasar yanki da ke ɓangaren hamayya.
2) Alƙawurra ga ƴansiyasa
Malam Kabiru Sufi ya kuma ce irin alƙawarin da shugaba Tinubu ke yi wa ƴan siyasa musamman masu alaƙa da ayyukan da za su samar da ci gaba a yankunansu.
Lokuta da dama waɗanda suka sauya sheƙar suna tabbatar da irin wannan iƙrarin cewa sun sauya sheƙar ne domin samun damar yi wa al’ummarsu aiki.
A wani ɓangaren kuma ana zargin gwamnatin ta APC da yi wa ƴan siyasa masu hamayya alƙawarin takara a mazaɓunsu da kuma muƙamai da ma samun damar yin walwala a zauren majalisa.
“Su ƴan siyasa a Najeriya duk halinsu guda ɗaya wato kura ki tsira da na bakinki. Da damar su ba sa iya yin azumi irin na siyasa wanda hakan ke sa su su sauya sheƙa zuwa ɓangaren gwamnati mai mulki.” In ji Dakta Mukhtar Bello Maisudan.
3) Kunna rikici a jam’iyyun hamayya
Dakta Mukhtar Bello Maisudan, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Bayero da ke Kano ya ce rikicin da jam’iyyun hamayya ke fama da shi na da alaƙa da sauya sheƙar masu hamayya.
“Idan ka kalli PDP ta zama mushen gizaka. Haka ma jam’iyyar LP ita ma an kunno mata rikici tsakanin ɓangarori biyu. Ita ma jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu.
Ba sabon abu ba ne. Idan jam’iyya na mulki to za ka ga za ta iya yin komai wajen goyawa wasu baya a cikin jam’iyyun hamayya domin rura musu rikici.” In ji Dakta Maisudan.
4) Amfani da tsoratarwa
Dakta Mukhtar Bello Maisudan ya ce a lokuta da dama jam’iyya mai mulki na amfani da wasu hukumomi wajen tsoratar da abokan hamayya da ke da tabo, inda ake nuna musu ko dai su koma jam’iyyar mai mulki ko kuma a yi musu bi-ta-da-ƙulli.
“Ana ganin kamar ita jam’iyya da shugaba Tinubu da magoya bayansa na amfani da wasu hukumomi ta hanyar amfani da tsaoratar da manyan ƴaƴan jam’iyyun hamayya da suka taɓa riƙe muƙamai a baya kuma suka yi wa-ka-ci wa-ka-tashi kuma ana riƙe da fayil-fayil ɗinsu.
Wannan zai iya jayowa a hura musu wuta cewa idan ba su goya wa shugaban ƙasa baya ba to za a yi musu bita da ƙulli – ba lallai mutum ya sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ba. Zai iya zama a inda yake amma zai bayar da goyon baya.” In ji Dakta Maisudan.
‘Wannan ne sauyin sheƙa mafi girma’
Malam Kabiru Sufi ya ce irin sauyin sheƙar da ake gani a wannan jamhuriyar ta huɗu ita ce mafi girma a tarihi da Najeriya ta taɓa fuskanta.
“Gaskiya batun samun tsallakawa zuwa jam’iyya mai mulki ba a taɓa samun irin na yanzu ba. Sai dai kawai za a iya cewa jam’iyyar PDP lokacin da ta yi sharafinta ta fi APC ƙarfi domin a 2007 jam’iyyar PDP na da jihohi 29 daga 36 na ƙasar.
Kenan za a iya cewa duk da APC ba ta kai tagomashin da PDP ta samu a baya ba amma kuma tafi kafa tarihin zawarcin abokan hamayya komawa jam’iyya mai mulki. Ba a samu irin wannan tururuwar sauya sheƙa ba a jamhuriya ta ɗaya da ta biyu da ta uku sai yanzu a ta huɗu.” In ji Malam Kabiru Sufi.