
“Duk shikashika da za su jawo rage farashin man fetur an cika su a yanzu,” kamar yadda Farfesa Ahmed Adamu – masanin tattalin arzikin man fetur a jami’ar Nile University da ke Abuja – ya shaida wa BBC.
Gasa
Tun bayan sauye-sauyen da aka samu a kasuwar hada-hadar man fetur ta Najeriya, aka fara samun gasa tsakanin masu shigo da man da kuma matatar Dangote.
Wannan gasa na ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo raguwar farashin, ko kuma sanadiyyar hana farashin ya ƙaru.
“Da ma amfanin gasa kenan. Shi Dangote yana ganin yanzu yana yin takara ne da wasu matatun man fetur ɗin na duniya, kuma babban burinsa shi ne ya riga kowa sayarwa,” in ji Farfesa Ahmed.
“Da zai yiwu ma, zai so ya haddasa yadda za a yi wasu ‘yankasuwar ma su ji ba za su iya ci gaba da harkar ba, ta yadda duk masu sari za su tsallake kowace matata su saya a wajensa.
“Shi ya sa ma shi kansa kamfanin NNPC yakan sayi man a wajen Dangote, duk da cewa yana shigo da man daga waje.”
Ɗaya daga cikin sharuɗɗan kasuwanci tsakanin Dangote da ‘yankasuwa shi ne dole ne dillali ya sayi abin da bai gaza lita miliyan biyu ba, kuma babu mamaki wannan ne ya sa ƙananan ‘yankasuwa ba su iya sayen man nasa.
Farfaɗowar darajar naira
‘Yar farfaɗowar da darajar kuɗin naira ya yi na daga cikin abubuwan da ka iya jawo raguwar man fetur ɗin na Dangote.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an fara ganin raguwar darajar dalar ne tun daga farkon watan Fabrairu a hukumance da kuma kasuwannin bayan fage a Najeriya.
“Harkar canjin kuɗin ƙasashen ƙetare na cikin manyan abubuwan da suka fi shafar farashin man fetur,” a cewar Farfesa Ahmed Adamu.
Dalili a nan shi ne, gwamnatin Najeriya na sayar wa matatar ta Dangote ɗanyen man fetur a naira maimakon dalar Amurka.
“Ba wai sauƙi aka yi masa ba, farashin ɗanyen fetur ɗin ake aunawa a kasuwar duniya, sai a canza shi zuwa naira, shi kuma Dangote ya biya da nairar,” kamar yadda Farfesa Ahmed Adamu ya yi bayani.
“Hakan na nufin nairar da Dangote zai biya wajen sayen ɗanyen man ta ragu, wanda zai sa shi kuma ya rage farashin da yake bai wa masu sari.”
Karyewar farashin ɗanyen mai
Wani dalilin shi ne na karyewar darajar ɗanyen man fetur a kasuwar duniya.
Bayanai sun nuna cewa samfurin Brent da Najeriya ta fi amfani da shi kuma take jingina farashi a kansa ya karye zuwa dala 73.92 kan kowace ganga ɗaya daga 74.29 a makon da ya wuce.
“Tun da aka shigo wannan shekara bai taɓa yin ƙasa ba kamar yanzu. A watan Janairu ya kai kusan dala 81,” in ji Farfesa Ahmed.
“Da a ce mutum ɗaya ne a kasuwar, babu gasa, sai ya yi shuru kawai ya ci gaba da cin kasuwarsa yadda yake so.”
Azumin Ramadana
A nata ɓangaren, matatar mai ta Dangote ta ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ta rage farashin man har da shirin da al’ummar Musulmi ke yi na fara ibadar azumin watan Ramadana.
Ana sa ran za a fara azumin a ranar Asabar ko Lahadi, inda Musulami kan shafe tsawon wuni babu ci babu sha tsawon kwana 29 ko 30 a jere.
“An ɗauki matakin ragewar ne domin sauƙaka wa ‘yan Najeriya saboda shirin fara azumin Ramadana, da kuma tallafa wa gwamnatin Tinubu game da tsarinta na farfaɗo da tattalin arziki…,” a cewar sanarwar da ta fitar ranar Laraba.